Home Labaru FRSC Ta Karyata Fara Amfani Da Dokokin Shari’a Wajen Hukunta Masu Karya...

FRSC Ta Karyata Fara Amfani Da Dokokin Shari’a Wajen Hukunta Masu Karya Doka

220
0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Nijeriya FRSC, ta nesanta kan ta
daga rahotannin da ke cewa ta na shirin fara amfani da
dokokin shari’ar musulunci wajen hukunta masu karya
dokokin tuƙi.

A cikin wata sanarwa dauke sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Bisi Kazeem, hukumar ta ce labarin ba ya da alaƙa da ita.

A makon da ya gabata ne, wasu jaridun Nijeriya su ka ruwaito wani kwamandan hukumar ya na kira da a fara amfani da dokokin shari’ar musulunci ga masu karya dokokin tuƙi.

Kwamandan ya ce dokokin hukumar sun gaza ta fuskar hukunta masu laifuffukan, don haka ya bukaci hukumar ta fara amfani da dokokin shari’ar musulunci.

Sai dai a sanarwar hukumar ta fitar, ta ce babban kwamandan hukumar na ƙasa Dauda Ali Biu ya umarci kwamandan da ya yi wannan furucin ya bayyana a helkwatar hukumar da ke Abuja, domin a cewar sa, kalaman kwamandan sun saɓa wa dokokin hukumar.

Sanarwar ta ce dokoki da ƙa’idojin da su ka kafa hukumar ba dokoki ba ne na wani addini ko wani yanki a Nijeriya ba, don haka hukumar ta bukaci al’umma su yi watsi da furucin da jami’in ya yi.

Leave a Reply