Home Labaru Harin Offa: Kotu Ta Yanke Wa ’Yan Fashin Banki Hukuncin Kisa

Harin Offa: Kotu Ta Yanke Wa ’Yan Fashin Banki Hukuncin Kisa

27
0
Rataya
Rataya

Wata Babbar Kotun Jihar Kwara, ta yanke wa wasu mutum biyar da aka tuhuma da fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai Shari’a Haleema Salman, ta babbar kotun  da ke birnin Ilorin ta yanke wa mutanen biyar da aka zarga da fasa bankin Offa shekara shida da suka gabata hukuncin.

Kotun ta samu mutanen da laifin fashi da makami da kisan mutanen da ba su ji ba su gani ba, ciki har da jami’an ’yan sanda a lokacin mummunan harin.

Waɗanda hukuncin ya shafa sun haɗa da Ayoade Akinnibosun, da Azeez Salahudeen, da Niyi Ogundiran, da Ibikunle Ogunleye da kuma Adeola Abraham.

Jagoran lauyoyin da ke gabatar da ƙara, Rotimi Jacob mai mukamin (SAN), ya ce shekara shida da suka shafe domin tabbatar wannan tuhumar sun haifar da ɗa mai ido.

Shi ma lauyan masu kariya, Nathaniel Emeribe wanda Abdullahi Jumba ya wakilta, ya ce hukuncin da kotun ta yanke bai zo da mamaki ba la’akari da irin ƙwararan hujjojin da aka gabatar a yayin shari’ar.

Leave a Reply