Home Muryar 'Yanci Ambaliyar Ruwa: Mutum 11 Sun Mutu A Jihar Neja

Ambaliyar Ruwa: Mutum 11 Sun Mutu A Jihar Neja

10
0
Jigawa flood1
Jigawa flood1

Mummunar ambaliya ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum 11 a jihar Neja, tare da lalata garuruwa masu yawa a faɗin ƙananan hukumomi 19 daga cikin 25 da ke jihar.

Cikin wata sanarwa da daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba-Arah, ya fitar ya ce lamarin ya lalata gidaje fiye da 6,865, tare da gonaki 118,692,

Lamarin ya jefa fiye da mutum 41,000 cikin tsananin buƙatar tallafi.

Baya ga lalata gonakin, ambaliyar ta kuma shafi makarantu 246, lamarin da ya shafi harkokin ilimi a garuruwa 529 na jihar.

Ƙananan hukumomin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Mokwa, da Katcha, da Lavun, da Lapai, da Agaie, da Shiroro, da Munya, da Gbako, da Kontagora, da Bosso, da Edati, da Agwara, da Bida, da Magama, da Mashegu, da Borgu, da Gurara, da Suleja da kuma ƙaramar hukumar Rijau.

Rahotonni sun ce ambaliyar ta kuma shafi gadoji 18 da kwalbatoci 80, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri a wasu yankunan jihar.

Leave a Reply