Home Labaru Hanifa Abubakar: Matasa Sun Cinna Wuta A Makarantar Su Yarinyar Da Aka...

Hanifa Abubakar: Matasa Sun Cinna Wuta A Makarantar Su Yarinyar Da Aka Kashe A Kano

194
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce matasan sun kona makarantar ce da tsakar daren Litinin.

Sai dai ya kara da cewa kawo yanzu ba su kama wadanda ake zargi da aikata ta’asar ba.

A makon jiya ne aka gano gawar Hanifa wadda ake zargin mai makarantar Noble Kids School, Abdulmalik Tanko, ya sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

A yayin da aka gabatar da shi ga manema labarai, ya ce ya kashe ta ne bayan ya sanya mata shinkafar-bera a cikin shayi sannan ya gididdiba ta ya binne a wani rami da ya haka a makarantar.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama’a inda aka rika yin alla-wadai.

Gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar sannan ta sha alwashin hukunta mutumin da ake zargi da kisa kisan yarinyar.

Leave a Reply