Home Home Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Jihar Taraba

Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Jihar Taraba

200
0

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe aƙalla mutum uku a ƙauyen Wuro Bokki da ke Ƙaramar Hukumar GassoI ta Jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa aƙalla ƴan bindiga 12 ne suka kai harin a ƙauyen da misalin ƙarfe biyar da rabi na yammacin Asabar.

An ruwaito cewa mutum ukun da aka kashe duka yan uwan mai garin Wuro Bokki ɗin ne.

Wurro Bokki din bai da nisa daga Karal, wanda wuri ne da aka kashe jami’an sa kai sama da 30 makonni biyu da suka gabata.

Zuwa yanzu dai hukumomin ƴan sanda a jihar ba su ce komai ba dangane da wannan lamari.

Leave a Reply