Home Labaru Hangen Nesa: Saraki Ya Ce Matsalar Tsaro Na Da Nasaba Da Matsalar...

Hangen Nesa: Saraki Ya Ce Matsalar Tsaro Na Da Nasaba Da Matsalar Ilimi

319
0
Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce samar da ingantaccen ilmi na daya daga cikin muhimman matakan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro a cikin al’umma.

Saraki ya ce matsalar tsaro a Nijeriya da ma kowace al’umma, ta na da nasaba da kalubalen da fannin ilimi ke fuskanta.

Bukola Saraki ya bayyana haka ne, a wajen taron Kungiyar Shugabannin Majalisar Dattawa ta Duniya karo na 140 da ya gudana a birnin Doha na kasar Qatar.

Saraki ya ce muddin aka ba matasa ingantaccen ilmi, to za a dakile yawaitar matasa masu tsatstsauran ra’ayin da ke kai su ga shiga kungiyoyin ta’addanci.

Ya ce idan aka ginganta ilmi, al’umma tagari za ta wanzu tare da rayuwar zaman lumana da ci-gaban kasa, ya na mai cewa shirin Afuwar Shugaban Kasa ga tsagerun Neja Delta ya yi tasiri sosai, domin ya sama wa matasa guraben karatu tare da daukar nauyin su zuwa jami’o’i.

Leave a Reply