Home Labaru Kin Amincewa Da Dokoki 2: Majalisa Ta Ce Za Ta Yi Amfani...

Kin Amincewa Da Dokoki 2: Majalisa Ta Ce Za Ta Yi Amfani Da Karfin Iko A Kan Buhari

418
0

Majalisar dattawa ta amince da yin amfani da karfin ikon da ta ke da shi, na amincewa da kudirin da ke bukatar yi wa tsarin mulki da na bangaren kasuwancin man fetur garambawul, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu a kan su.

Kudirorin biyu dai su na daga cikin wadanda shugaba Buhari ya maida wa majalisa tare da bayanin dalilin sa na kin rattaba hannu a kan su.

Majalisar ta na bukatar kaso biyu cikin uku na adadin sanatocin Nijeriya kafin su iya yin amfani da karfin ikon su don tabbatar da dokokin biyu da shugaba Buhari bai amince da su ba.

Haka kuma, majalisar ta yanke shawarar yin gyara a kan wasu kudirori 11 domin sake maida su ga shugaba Muhammadu Buhari ya amince da su.

Majalisar, ta ce za ta yi watsi da kudirori hudu da shugaba Buhari ya ki sanya wa hannu, biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin adalci da Sanata David Umaru ke jagoranta da majalisar ta yi.6���Y<� �

Leave a Reply