Ministan lafiya Isaac Adewole, ya yi kira ga iyaye da dalibai ‘yan Nijeriya da ke so su yi karatun likitancin a jami’o’in da ke kasar Ukraine su binciki kwarewar makarantar da shaidar amincewa da digirin su kafin su tafi.
Adewole ya yi kiran ne, bayan sauraren kalaman da mininstan lafiya na kasar Ukraine ya yi cewa, ba ya da tabbacin ingancin ilimin da wasu jami’o’in da ke gabashin kasashen Turai ke koyarwa ba.
Ya ce ministan ya bayyana cewa, ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Ukraine ba ta da tabbacin ingancin ilimin da jami’ar Odessa National Medical University ke badawa
Adewole ya ce don haka ne ya ke kira ga iyaye da dalibai su yi bincike kafin su tura ‘ya’yan su zuwa wadancan jami’o’i.
You must log in to post a comment.