Home Labaru Hajjin 2019: Hukumar Alhazai Ta Ankarar Da Maniyyata Kan Ayyukan ‘Yan...

Hajjin 2019: Hukumar Alhazai Ta Ankarar Da Maniyyata Kan Ayyukan ‘Yan Damfara

347
0

Hukumar alhazai ta Abuja, ta ankarar da maniyyatan bana kan ayyukan ‘Yan damfara.

Shugaban hukumar Muhammad Bashir ya bayyana haka ga manema labarai a wani taron wayar da kai da aka shiryawa maniyyatan bana da kuma ma’aikatan hukumar a sansanin alhazai na dake filin jirgin sama na Abuja.

Hukumar ta ce ta shirya taron ne domin wayar da kan maniyyata da jami’an hukumar domin samar da yanayi mai kyau a tsakanin maniyyata da kuma jami’an hukumar alhazan.

Muhammad Bashir, ya ce ta hakan ne kadai hukumar za ta sami cimma nasarar gudanar da aikin  hajji, sannan kuma ya gargadi maniyyatan su zama jakadu na gari a kasar Saudiyya.

Ya kara da cewa taron na wuni guda zai kara tunatar da maniyyata da jami’an hukumar alhazan ayyukan da suka dauro a kansu, sannan zai kara wayar musu da kai, ta yadda za su kaucewa ayyukan mazambata a Nijeriya da kasar Saudiyya.

Leave a Reply