Rundunar ‘yan sanda Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa an sami barkewar rikicin kabilanci da na addini a wasu sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce guje-gujen da aka yi a Sabon-Tasha da Mararraban Rido ba su da wata alaka da rikicin kabilanci ko na addini, domin haka mutane su kwantar da hankulan su.
Ya ce Guje-gujen da aka yi, ya auku ne sakamakon kama wani barawon takalmi da aka yi a kasuwar Sabo, a daidai lokacin da ake kokarin kama barawon ne, aka sami guje-guje, mutane suka dauka rikici ne ya barke.
Kwamishinan, ya kara da cewa sakamakon guje-gujen ne aka fara yada yada jita-jita, a cikin garin Kaduna, ya ce ba komai bane illa koruruwar shaidan da wasu bata gari ke yadawa domin haifar da zaune tsaye a Kaduna. Ahmad Abdurrahman, ya ce tuni da jami’an tsaro na musamman suka fara sintiri domin kawar da dukkannin wata matsala da ka iya biyowa bayan jita-jitar.
You must log in to post a comment.