Home Labaru Gwamnan Taraba Ya Kafa Kwamiti Domin Ƙwato Kadarorin Gwamnati

Gwamnan Taraba Ya Kafa Kwamiti Domin Ƙwato Kadarorin Gwamnati

102
0

Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas, ya kafa kwamiti da zai yi
bincike tare da ƙwato kadarorin jihar a faɗin Nijeriya.

An dai ɗora wa kwamitin alhakin bincike da kuma gano kadarori a jihar Kaduna da ofishin jihar da ke Legas da birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Gebon Kataps ya fitar, ya ce an ɗora wa kwamitin nauyin nema da kuma gano inda kowane irin nau’in kadarorin gwamnatin su ke a faɗin Nijeriya.

Gebon Kataps, ya ce kwamitin zai kuma ƙimanta kuɗin kowace kadara sannan ya ba gwamnatin jihar shawarwari, kuma ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahoton sa cikin makonni huɗu.

Leave a Reply