Jam’iyyar APC, ta ce babu wanda ya tilasta wa Sanata
Abdullahi Adamu yin murabus daga shugabancin jam’iyyar.
APC ta bayyana haka ne, jim kadan bayan kammala taron shugabannin gudanarwa na jam’iyyar a Abuja.
Daraktan yada labarai na jam’iyar APC Bala Ibrahim, ya ce bisa radin kai Abdullahi Adamu ya mika takardar murabus, shi ya sa bai halarci taron zaben shugaban wucin gadi ba.
Tun farko dai masana harkokin siyasa sun dade da hango cewa ba za a samu jituwa tsakanin Sanata Abdullahi Adamu da shugaba Tinubu ba, sakamakon hannun rigar da su ka yi gabanin zaben fidda gwani na dan takarar jam’iyyar.