Home Labaru Ilimi Sarkin Musulmi Ya Ayyana Farkon Shekarar Musulunci Ta 1445

Sarkin Musulmi Ya Ayyana Farkon Shekarar Musulunci Ta 1445

175
0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad
Abubakar, ya ayyana Laraba, 19 ga watan Yuli na shekara ta
2023 a matsayin 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar
Musulunci ta 1445 bayan Hijira.

Kafin wannan lokaci, Basaraken ya buƙaci al’ummar Musulmi su nemi jinjirin watan Muharram a ranar Litinin da ta gabata.

Watan Muharram dai shi ne watan farko a kalandar Musulunci, kuma ɗaya daga cikin muhimman watannin da Musulunci ya ke ba fifiko.

A wannan watan ne, al’ummar Musulmin duniya ke yin azumin nafila a ranakun 9 da 10 ga watan, wato Tasu’a da Ashura don neman kusanci ga Allah Madaukakin Sarki.

Leave a Reply