Home Labaru Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Agwam Adara...

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Agwam Adara A Kaduna

906
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kama wani mutum mai suna Abubakar Ibrahim mai shekaru 37 wanda take tuhumar da zargin kashe Agwam Adara Maiwada Galadima.

Mai magana da da yawun rundunar yan sandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana haka, inda ya ce sun kama Salisu ne a garin Rigachikun dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Sanarwar ta kara da cewa Salisu da kansa ya amsa aikata laifin yin garkuwa da Galadima, tare da kashe shi, bugu da kari ya bayyana yadda shi da wasu abokan aikinsa suke satar mutane a Kaduna.

Frank Mba, ya ce ‘yan sanda sun sami nasarar kama wasu gungun barayin mutane su goma sha takwas bayan sun kama shugabansu, kuma babban malamin tsubbun dake ba su sa’a mai suna Salisu Abubakar.

Yan sandan sun yi sa’ar bankado sansanonin barayin daban daban da suka hada da na Birnin Gwari da Rijana da Katari Mai Daro da kuma Dajin Buruku, duk a cikin jahar Kaduna.

A watan Oktobar bara ne yan bindiga suka yi garkuwa da marigayi Agwam Adara Maiwada Galadima, inda daga bisani kuma suka kashe shi duk da cewa an biya su kudin fansa.

Leave a Reply