Home Labaru Yajin Aikin: Buhari Ya Nuna Takaicin Sa

Yajin Aikin: Buhari Ya Nuna Takaicin Sa

289
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ke yawan yajin aiki.

Shugaba kasa wanda ya sami wakilcin shugaban hukumar kula jami’o’in ta Najeriya, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayyana  hakan ne a lokacin da jami’ar Ahmadu Bello Zaria ke bikin yaye dalibai.

Buhari, ya ce duk wani yajin aiki da kungiyar malamai suka gudanar  na gurgunta ci gaban karatu, tare da gurgunta tsare tsaren jami’iar kanta.

Shugaba Buhari ya nemi kungiyoyin malaman jami’a da sauran kungiyoyin dake jami’a su kasance masu la’akari da bukatun wasu ba wai nasu kadai ba, a duk lokacin da suke tunanin shiga yajin aiki.

Haka zalika shugaban kasa ya jinjina wa jami’ar Ahmedu Bello ta Zari’a akan  yadda take fadada ayyukanta, da suka hada da samar da tsarin samun ilimi daga nesa da hadin gwiwa da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi daban daban.

Leave a Reply