Home Labaru Nasara: Rundunar Sojan Ruwa Ta Cafke Sojojin Gona 19

Nasara: Rundunar Sojan Ruwa Ta Cafke Sojojin Gona 19

948
0

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta cafke wasu sojojin gona 19  a farkon shekara ta 2019.

Mai magana da yawun rundunar jami’an ruwa, Commodore Suleman Dahun, shi ne ya sanar da hakan lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya.

Commodore Suleman, ya ce sun yi nasarar kama mutane 19, wadanda ke aikata laifin Sojan gona garin  Kalaba a Yenogoa da kuma jihar Legas.

Ya ce yawanci an kama masu aikata laifuka ne da shaidar aikin sojin ruwa da jabun ID Card sannan kuma suna amsa sunan jami’an tsaro.

Ya gargadin jama’ar yankin  su kaucewa amfani da kayan jami’an tsaro matukar ba sa aiki da su, saboda an sami wasu bata gari na fakewa da aikin suna karban  kudaden mutane.

Ya sanar da cewa sa kayan jami’an tsaro da sunan sojan gona ya haramta, kuma duk wanda aka da laifi za a hukunta shi karkashin sashe na 109, da kuma 110 da na 251 a karkashin hukuncin doka.

Leave a Reply