Home Labaru Gargadi: Rasha Ta Janye Daga Yarjejeniyar Daina Kera Makaman Nukiliya

Gargadi: Rasha Ta Janye Daga Yarjejeniyar Daina Kera Makaman Nukiliya

496
0

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasar ta kammala janyewa baki daya daga yarjejeniyar daina kera makaman nukiliya da ta kulla tun shekarar 1987 tsakaninta da Amurka.
Shugaban Rasha,Vladmir Poutine, ya yi gargadin cewa rashin yarjejeniyar zai iya kasancewa bala’i ga Duniya.
Putin wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Saint Petersburg, na kasar Rasha gabanin taron tattalin arziki na duniya, ya ce Rasha na a shirye domin tattaunawa tare da samar da sabuwar yarjejeniya bayan rugujewar wadda aka kulla a shekara ta 1987 saboda zaman lafiyar duniya.
A watan oktoban shekarar 2017 ne Amurka ta ce, ba ta da niyyar sanya hannu kan yarjejeniyar haramta mallakar makamin nukiliya wadda ta samu goyon bayan kasashen duniya 122 a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
A cewar Amurka, yarjejeniyar ba za ta taka wata muhimmiyar rawa ba wajen tabbatar da zaman lafiya ko kuma inganta sha’anin tsaro a duniya.

Leave a Reply