Home Labaru Diplomasiyya: Venezuela Ta Bude Kan Iyakar Ta Da Colombia

Diplomasiyya: Venezuela Ta Bude Kan Iyakar Ta Da Colombia

277
0

Bayan share watanni ana gudanar da zanga-zanga a Venezuela Shugaban kasar Nicolas Maduro, ya umurci a sake bude kan iyakar kasar da Colombia a yankin Tachira dake yammacin kasar.
A watan Fabrairu bana ne Shugaban kasar ya dau mataki na rufe dukkannin kan iyakokin kasar na sama, da na ruwa, da na kasa da wasu tsibirai dake raba iyaka da kasar sa, biyo bayan rikicin siyasa da ya kuno kai tun bayan da Juan Gaido, ya ayana kan sa a matsayin Shugaban kasar ,lamarin da ya haifar da tarzoma.
Kasashen duniya na ci gaba da kira zuwa ga ‘yan siyasar Venezuela don ganin sun cimma matsaya ta gari da nufin dawo da doka da oda, yayinda wasu rahotanni ke cewa kusan mutane milyan daya ne suka gudu daga kasar zuwa wasu kasashe saboda rashin tsaro.