Home Labaru Adawa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke A Kamaru

Adawa: Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke A Kamaru

401
0

A kasar Kamaru duk da sallamar wasu mutane dari daga cikin magoya bayan jam’iyyar adawa ta MRC 351 da aka kama a yankuna daban-daban na kasar yayin zanga-zanga a ranar 1 ga watan Yuni, magoya bayan jam’iyyar sun ce suna kan bakar su na sake gudanar da wata zanga-zanga tare da gayyatar magoya bayan su a wata zanga-zangar gama gari.
A makon da ya gabata, Firaministan kasar ya kaddamar da wata ziyara zuwa yankunan ‘yan aware da nufin ganawa da Shugabanin kabilu tare da kokarin warware rikicin kasar.
‘Yan adawan na fatan gwamnati za ta sako jagoran su Maurice Kamto, shugaban jam’iyyar, kuma dan takara da ya yi ikirarin lashe zaben da ya gabata da wasu magoya bayan sa dake tsare a gidan kason Kundengui a birnin Yaounde.

Leave a Reply