Majalisar Dattawa ta amince da dokar da ta tsaida ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin sabuwar ranar dimokuradiyya sabanin yadda yake ranar 29 ga watan Mayu a baya.
Matakin majalisar na zuwa ne bayan akalla shekara guda da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana sauya ranar Dimokuradiyar ta Najeriya.
A zaman da ta yi majalisar ta dattawa ta sanya hannu kan wannan kudiri, wanda majalisar wakilai ta amince da shi tun a watan Disambar shekarar 2018. A zaman bisa jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekweremadu, majalisar ta yi amanna da sabon kudirin, yayin da shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawal, ya yi fashin baki kan manufar shugaban kasa.
You must log in to post a comment.