Home Labaru Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa: Gwamnonin Arewa Za Su Kashe Naira...

Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa: Gwamnonin Arewa Za Su Kashe Naira Biliyan 6

1147
0

Kungiyar Gwamnonin Arewa NSGF ta kafa wani Asusu da zata tara Naira milyan dubu 6 domin kaddamar da shirin farfafo da tattalin arzikin yankin.

Shugaban Kungiyar, kuma gwamnan jihar Borno Kashin Shettima, ya tabbatar da haka bayan kammala wani taron kungiyar a Kaduna.

Shettima ya ce an yi wannan hobbasa ne domin yankin Arewa ya samu wani ginshikin dogaro da a kai a fannin inganta tattalin arzki.

Ya cigaba da cewa a karkashin wannan shiri za a farfado da kamfanin masakar Arewa watau Arewa Textile da kuma kamfanin NNDC.

Ya ce jihohin Arwa ne ake sa ran za su bayar da gudummawar wadannan kudade, inda ya ce ya zuwa yanzu dai an tara naira miliyan 650. Da ya koma kan maganar matsalar tsaro kuwa, Shettima, ya ce a matsayin su na kungiya, gwamnonin Arewan sun kirkiro hanyoyi da matakai da da dama domin dakile matsalar tsaro a Najeriya.