Home Labaru Tsaro: Hukumar DSS Ta Saki Shahararren Malamin Musulunci Da Ta Kama A...

Tsaro: Hukumar DSS Ta Saki Shahararren Malamin Musulunci Da Ta Kama A Bauchi

547
0

Rundunar tsaro ta farin kaya DSS, ta saki shahararren malami Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da ta tsare bayan ya amsa wasu tambayoyi da ta yi masa.

Malam Abdulaziz, wanda ya shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, ya shiga hannun hukumar DSS ne a ranar Juma’a ta makon da ya gabata.

Daya daga cikin ‘daliban malamin Muhammad Abdulkadir ya tabbatar da sakin Malamin, ya na mai cewa kamun da aka yi wa Malamin zai kara ma shi daukake ne a idon duniya ba wai tauye kimar sa ba.

Sai dai ya ce har yanzu ba su da wata masaniya a kan ko hukumar ta gindaya wa Malamin na su wasu sharuda, amma ya tabbatar da sakin sa kuma tuni ya koma cikin iyalan sa lafiya. Idan dai za a iya tunawa, kimanin kwanaki biyar da su ka gabata ne hukumar DSS ta gayyaci Ustza Idris zuwa ofishin ta da ke Bauchi domin amsa tambayoyi, amma daga bisani su ka yi awon gaba da shi zuwa Abuja don ci-gaba da yi ma sh tambayoyi.

Leave a Reply