Home Labaru Daukar Ma’aikata: Rundunar Sojin Ruwa Ta Bayyana Ranar Da Za A Zana...

Daukar Ma’aikata: Rundunar Sojin Ruwa Ta Bayyana Ranar Da Za A Zana Jarabawa

376
0

Rundunan sojin ruwa ta Nijeriya, ta ce za ta gudanar da jarabawar daukar ma’aikata na shekara ta 2019 a ranar 13 ga watan Afrilu a cibiyoyi 30 da ke fadin Nijeriya.

Kakakin rundunar sojin ruwa Commodore Suleman Dahun ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce rundunar ta na burin sanar da al’umma cewa za ta gudanar da jarabawar gwaji ta daukar ma’aikata.

 Ya ce ana sa ran masu neman aikin za su bayyana da misalin karfe 8:00 na safiya a cibiyoyin da sunayen su su ka fada yayin da su ka yi rijista a yanar gizo.

A wani lamari makamancin haka, Makarantar horar da sojoji ta Kaduna NDA ta sanar da cewa, ta dakatar da zana jarabawar shiga makarantar ga daliban zango na 71.

Jami’in hulda da jama’a na makarantar Abubakar Abdullahi ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kaduna.

Ya ce a yanzu an dakatar da jarabawar, wadda aka shirya zanawa a ranar 13 ga watan Afrelu, amma za a sanar da sabuwar ranar da za a sake gudanar da jarabawar.

Leave a Reply