Kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara kan yaki da sha da fataucin Miyagun kwayoyi, ya sha alwashin yin dukkan mai yiwuwa wajen magance wannan matsala a fadin Nijeriya.
Shugaban Kwamitin Buba Marwa ya bayyana haka, a lokacin da ya jagoranci tawagar Kwamitin zuwa jihar Kaduna.
Buba Marwa, ya ce shugabannin al’umma da su ka hada da masu Unguwanni da Sarakuna da Malaman addinai, su na da rawar da za su taka wajen magance wannan matsala.Ya ce kwamitin da yanzu haka ya ke aiki a duk fadin Nijeriya, zai tabbatar da ya lalubo hanyoyin da su ka dace a bi domin hana sha da kuma fataucin Miyagun kwayoyi.