Home Labaru Dambarwar Siyasa: Gwamna: Okorocha Ya Ziyarci Buhari A Fadar Sa Da Ke...

Dambarwar Siyasa: Gwamna: Okorocha Ya Ziyarci Buhari A Fadar Sa Da Ke Abuja

347
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha a fadar sa da ke Abuja.

Gwamna Okorocha wanda jam’iyyar APC ta dakatar da shi a kan zargins a da yi wa jam’iyyar zagon kasa, ya isa fadar shugaban kasa ne inda da kai tsaye ya shige ofishin shugaban kasa Buhari.

Gwamnan, wanda kuma shi ne zababben sanatan mazabar Imo ta yamma na fuskantar kalubale daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a kan hana shi takardar shaidar cin zabe.

Kawo yanzu dai, hukumar ba ta ba gwamna Okorocha takardar shaidar cin zaben san a sanata ba, sakamakaon yadda babban jami’ain hukumar inec ya ce an tilastashi ne wajen bayyana sakamakon zaben.