Home Labaru Rabon Mukamai: Daruruwan Mata Sun Tattaru A Kofar Majalisar Dokokin Najeriya

Rabon Mukamai: Daruruwan Mata Sun Tattaru A Kofar Majalisar Dokokin Najeriya

312
0

Daruruwan Mata a karkashin kungiyoyi, sun gudanar da tattaki a babban birnin tarayya Abuja tare da mika bukatar a basu karin mukaman gwamnati.

Matan sun yi tattakin ne tare da wake-waken cewa suna bukatar a basu kashi hamsin cikin dari na mukamai a lokacin da daruruwan su daga jihohi 36, ciki har da birnin tarayya suka yi wani jerin gwano daga dandalin Eagle Square zuwa kofar majalisar dokoki a karkashin wata hadakar kungiya.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Binta Kasimu, ta ce sun zo majalisar ne domin su bayyana bukatun su na neman mukamai, kuma a ganinta mata sun cancanta tun da dama cancanta a ke so ba dauki-dora ba.

Ita kuma tsohuwar shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa Evelyn Onyilo, ta ce har yanzu a Najeriya babu mata da suka kai kashi talatin da biyar cikin dari, saboda haka dole ne a yi adalci a nada mata a gwamnati mai jiran gado. Daya daga cikin wadanda suka yi tattakin, Maryam Aliyu Abdullahi, ta ce sun je majalisar ne domin a nan ne suke da wakilan da zasu ji kukan su, ta kuma nemi wakilan su dube su da idon rahama a ba su abinda ya dace.