Home Labaru Da Dumi-Dumi: Wani Abun Fashewa Ya Fashe Ya Kashe Mutane 4 A...

Da Dumi-Dumi: Wani Abun Fashewa Ya Fashe Ya Kashe Mutane 4 A Sokoto

1
0

Akalla mutane hudu aka tabbatar da mutuwar su, yayin da
wasu uku su ka samu munanan raunuka sakamakon fashewar
tukunyar Gas a wani shagon walda da ke karamar hukumar
Isa ta jihar Sokoto.

Wani mazaunin unguwar, ya ce lokacin da ya ji karar fashewar wani abu mai karfi abin da ya fado ma shi a rai shi ne ‘yan bindiga ne su ka kai hari, amma da ya ga mutane su na gudu zuwa shagon waldar sai hankalin shi na kwanta.

Mutumin ya cigaba da cewa, da ya bincika sai ya samu labarin wani abun fashewa ne ya fashe a shagon mai walda, kuma an rasa rayuka yayin dawasu da dama su ka jikkata.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Sokoto DSP Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.