Home Labaru Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Manoma 9, Suka Sace 3 A Kaduna

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Manoma 9, Suka Sace 3 A Kaduna

51
0

‘Yan bindiga sun kashe manoma tara, tare da yin garkuwa da
wasu uku a Unguwar Danko da ke kusa da kauyen Dogon
Dawa a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce manoman su na aikin gonakin su ne, kwatsam ‘yan bindigar su ka fara harbin duk wanda su ka gani.

Zababben dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kakangi Yahaya Musa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce duk wadanda aka kashe manoma ne, kuma wadanda su ka samu raunukan harbin bindiga an garzaya da su asibiti domin yi masu magani.

Ya ce an tabbatar ma shi cewa ‘yan bindiga sun kashe manoma tara a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a ranar Asabar da ta gabata, wasu kuma sun tsira da raunukan harbin bindiga.

Leave a Reply