Home Labaru Hausawa Sun Zargi ’Yan Kabilar Kutep Da Kashe Musu Mutane A Kauyen...

Hausawa Sun Zargi ’Yan Kabilar Kutep Da Kashe Musu Mutane A Kauyen Taraba

66
0

Al’ummar Hausawa mazauna garin Takum a Jihar Taraba,
sun zargi dakarun Sa-Kai na ‘yan kabilar Kutep da hallaka
mutanen su da dama.

Wani Bahaushe mai suna Yakubu Sani ya shaida wa manema labarai cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun kai hari a unguwannin Hausawan da ke garin Takum, kuma ko kadan mutanen su ba su tsokani wani ko wata kabila a yankin da zai sa a kai masu hari har a hallaka masu mutane ba.

Yakubu Sani ya kara da cewa, Hausawa ba su cikin rigimar da ke tsakin ‘yan kabilar Kutep da Fulani, amma sai ga shi an huce hushi a kan su.

Ya ce dakarun sa-kai na ’yan kabilar Kutep sun kashe Hausawa matafiya 13 a kan hanyar Takum zuwa Maraba da kuma hanyar Takum zuwa Kashinbila.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar SP Usman Abdullahi, ya ce ‘yan kabilar Kutep sun kashe Hausawa biyu, wanda hakan ya harzuka Hausawa kuma rigima ya tashi a garin na Takum, ya na mai cewa tuni an tura sojoji da ‘yan sanda a garin domin kawo karshen rigimar.

Leave a Reply