Home Labaru Dole IG Adamu Da Abba Kyari Su Bayyana A Kotu

Dole IG Adamu Da Abba Kyari Su Bayyana A Kotu

381
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Jos na jihar Filato, ta umurci shugaban rundunar ‘yan snadan Nijeriya Mohammed Adamu da Shugaban da shugaban tawagar tattara bayanan sirri Abba Kyari su bayyana a gaban ta domin bada bayyanin da zai hana a tuhume su da laifin raina kotu.

DCP Abba Kyari, Shugaban Tawagar Tattara Bayanan Sirri Na Rundunr 'Yan Sanda
DCP Abba Kyari, Shugaban Tawagar Tattara Bayanan Sirri Na Rundunr ‘Yan Sanda

Mai shari’a Dorcas Agishi ta bada umurnin ne, yayin da ta ke sauraren karar da aka shigar a kan wani Nanpon Sambo na Ma’aikatar Shari’a da jami’an tsaro na farin kaya SSS su ka shigar bisa tuhumar sa da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

Wata majiya ta ce, an gurfanar da Sambo ne bisa tuhumar sa da laifin mallakar makamai ba bisa ka,ida ba, amma jim kadan bayan zaben shugaban kasa aka ce ‘yan sandan tawagar Abba Kyari sun yi awon gaba da shi.

Yayin da za a cigaba da sauraren shari’ar, lauyan Sambo Daniel Dashe, ya ce bai sake ji daga wanda ya ke karewa ba, kuma iyalan sa ma ba su san inda ya ke ba.

Dashe ya shaida wa kotun cewa, bacewar Sambo ta na kawo cikas ga shari’ar da ake gudanarwa, kuma ya bukaci kotu ta dauki mataki kan shugaban ‘yan sandan Nijeriya da Abba Kyari, bisa zargin saba umurnin kotu da gangan na tsare Sambo tun ranar 3 ga watan Afrilu da su ka yi awon gaba da shi.

Leave a Reply