Home Labaru Boko Haram: UNICEF Ta Koka A Kan Amfani Da Yara Wajen Kai...

Boko Haram: UNICEF Ta Koka A Kan Amfani Da Yara Wajen Kai Hare-Hare

337
0

Hukumar tallafa wa kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF, ta yi Allah-Wadai da yadda kungiyar Boko Haram ke amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake a Nijeriya.

UNICEF ta bayyana haka ne, yayin da ta ke raddi a kan hare-haren kunar-bakin-waken da Boko Haram ta kai a wani gidan kallo da ke garin Konduga, inda mutane 30 su ka hallaka, sama da 40 kuma su ka jikkata.

Mazauna garin da su ka shaida faruwar lamarin, sun ce wasu kananan yara uku ne su ka kai harin na Konduga, biyu daga cikin su mata da kuma namiji daya.

Hukumar UNICEF, ta ce harin na Konduga ya sa adadin kananan yaran da kungiyar Boko Haram ta yi amfani da su wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake ya kai biyar, daga farkon shekara ta 2019 zuwa yanzu.

A wani rahoto da UNICEF ta fitar a shekara ta 2018, ta ce kananan yara 48 Boko Haram ta yi amfani da su wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake, daga cikin su kuma yara mata 38 ne.