Home Labaru Kyawawan Dabi’u: Buhari Ya Jinjina Wa ‘Yan Nijeriya Mazauna Kasashen Ketare

Kyawawan Dabi’u: Buhari Ya Jinjina Wa ‘Yan Nijeriya Mazauna Kasashen Ketare

394
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa ‘yan Nijeriya  mazauna kasashen ketare a kan yadda su ke gudanar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Buhari ya yi wannan yabo ne a lokacin da tawagar kungiyar jakadun Nijeriya karkashin jagorancin Kwamared Jasper Emenike su ka kai masa ziyara a  fadar sa da ke Abuja.

Shugaban kasa Buhari ya kuma gargadi ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen ketare su kasance masu son zaman lafiya da a kasashen da suka samu karamci.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa a Femi Adesina ya fitar, inda ya bayyana farin cikin sa a kan wannan ziyara da ‘yan kungiyar jakadun Nijeriya su kai masa, tare da yaba masu akan yadda su ke kare martabar Nijeriya a idon duniya.

A nashi jawabin, jagoran tawagar Jasper Emenike ya mika godiyar tare da taya shugaban kasa Buhari murnar samun nasara ta lashe zabe a karo na biyu, sannan  ya yabawa kwazon shugaba Buhari na yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta hanyar shimfida tsare tsare masu tasiri a yaki da rashawa.

Leave a Reply