Home Labaru Ilimi: Yara Miliyan 8 Ba Su Zuwa Makarantar Boko A Jihohin Nijeriya...

Ilimi: Yara Miliyan 8 Ba Su Zuwa Makarantar Boko A Jihohin Nijeriya 10 – UNICEF

426
0

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce yanzu haka kananan yara miliyan 8 ne ba su zuwa makarantar Boko a Jihohin Nijeriya 10 da birnin tarayya Abuja.

A cikin wata sanarwa da wakilin UNICEF a Nijeriya Peter Hawkins ya fitar, ta bayyana jihohin Bauchi da Neja da Katsina da Kano da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Gombe da Adamawa da kuma Taraba, a matsayin wadanda su ke fama da wannan matsala.

Hawkins, ya ce yanzu haka wasu matasa 2,000 sun sanya hannu a kan takardar korafi, su na bukatar shugabannin jihohin 10 su tabbatar an ba wadannan yara ilimi mai inganci, musamman mata.

Jami’in ya ce, tashe-tashen hankulan da ake samu a yankin arewacin Nijeriya, ya hana yara miliyan 10 da rabi samun ilimi mai inganci, yayin da rikicin Boko Haram ya haifar da lalata makarantu da kashe malamai da kuma tsorata iyaye tura yaran su zuwa makaranta.