Home Labaru Boko Haram: Mutane 3 Sun Mutu, 45 Sun Jikkata A Wani Harin...

Boko Haram: Mutane 3 Sun Mutu, 45 Sun Jikkata A Wani Harin Kunar Bakin Wake A Borno

390
0

Wasu hare-haren kunar bakin-wake guda biyu sun yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an sa-kai biyu, da farar hula guda daya tare da jikkata wasu mutane 45 a garin Muna Dalti da ke Maiduguri a jihar Borno.

Shugaban tawagar kai agaji na hukumar bada agajin gaugawa ta jihar Borno Bello Dambatta ya tabbatar da faruwar harin da aka kai a daren ranar Asabar da ta gabata.

Dabatta, ya ce jami’an sa-kai sun hango ‘yan kunar-bakin-waken dauke da abubuwan fashewa a jikin su, inda su ka yi kokarin dakatar da su, amma su ka tada boma-boman da su ka yi sanadin mutuwar ‘yan kunar-bakin-waken tare da jami’an sa-kai.
‘Yan kunar-bakin-waken biyu wadanda dukkan su mata ne, sun tada boma-boman da ke jikin su ne bayan tazarar mintuna biyar a garin Muna Dalti.

Ya ce wadanda su ka jikkatan sun samu raunuka da dama sakamakon fashewar boma-boman, wadanda ke samun kulawa daga likitoci a babban asibitin Maiduguri.

Leave a Reply