Rundunar mayakan sojan sama ta Najeriya ta yi amfani da jiragen yaki wajen yi wa ‘yan bindigar ruwan harsasai a mabuyar su dake dazukan jahar Zamfara.
Mai Magana da yawun rundunar, Iya komodo Ibikunle Daramola, ne ya bayyana haka, ya ce Sojojin sun kai harin ne a karshen makon da ya gabata bayan samun bayanan sirri dake tabbatar musu da taruwar ‘yan bindiga a mafakarsu.
Ya ci gaba da cewa rundunar ta sake turawa da wani jirgin yakin Najeriya kirar Alpha Jet zuwa wani gida da ‘yan bindigar suka fake a ciki, inda jirgin ya kona gidan gaba daya ta hanyar jefa masa bama-bamai, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga da dama. Cikin wani bidiyo da rundunar ta yada a kafafen sadarwa, an hangi yadda jiragen yaki sun halaka wasu yan bindiga da suke tserewa a kafa suna neman mafaka, wasu kuma aka bi su kauyen Wanoke kafin daga bisani aka hallaka su.
You must log in to post a comment.