Kotun daukaka kara da ke Garin Akure a jihar Ondo, ta tabbatar da cancantar takarar gwamnan jihar Osun da Sanata Ademola Adeleke ya yi har ake ikirarin ya lashe zabe.
Babban kotun dai ta rusa hukuncin da wani Alkalin kotun tarayya ya yi a Abuja, wanda ya zartar da cewa Ademola Adeleke bai cika sharuddan da ake nema wajen tsayawa takarar kujerar Gwamna a Nijeriya ba.
Sai dai alkali A. Danjuma ya yi watsi da wannan hukunci na kotun tarayya, inda ya amince da rokon dan takarar gwamnan, ya kuma soke matakin da karamar kotun ta dauka a makon da ya gabata a kan wasu manyan dalilai uku.
Daga cikin dalilan da Alkalin kotun daukaka karar ya bada kun sun hada da, tun farko kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraren karar a kan Ademola Adeleke da wani Kingsley Awosiyan ya kai mata har ta kai ga rusa takarar Sanatan.
Sauran Alkalan da su ka yanke wannan hukunci a zaman da aka yi sun hada da mai shari’a R.A Abdullahi da kuma P.A Mahmoud.
You must log in to post a comment.