Home Labaru Bayan Ziyarar Maiduguri: Shugaban Kasa Buhari Ya Tafi Hutu Kasar Ingila

Bayan Ziyarar Maiduguri: Shugaban Kasa Buhari Ya Tafi Hutu Kasar Ingila

309
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar ingila bayan ya kammala ziyarar aiki a jihar Borno.

Idan dai ba a manata ba, a kwanakin baya ne mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce shugaba Buhari zai je hutu kasar Ingila bayan kammala ziyarar aiki a jihar Borno.

Ana dai sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dowa Nijeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu, kwanaki 17 zuwa ranar da zai rushe dukkanin mukaman siyasar da ya nada.

Shugaban kasa Buhari zai rushe masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin sa a ranar 22 ga watan Mayu, bayan ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya, kamar yadda ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad ya tabbatar.

Lai Muhammad ya sanar da haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da ta gudana a fasar shugaban kasa da ke Abuja.

Leave a Reply