Home Labaru Ziyarar Maiduguri: Buhari Ya Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka A Jihar Borno

Ziyarar Maiduguri: Buhari Ya Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka A Jihar Borno

357
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima.

Daga cikin ayyukan da shugaban kasa Buhari ya kaddamar sun hada da tarin wasu gidaje 246 da kashim shattima ya gina a Maiduguri babban birnin jihar.

Haka kuma gwamna Kashim Shettima ya gina wata makarantar firamare a Maiduguri da ka sa wa suna Babagana Kingibe.

Gwamnatin jihar Borno dai, ta zabi ta karrama jakada Babagana Kingibe ne sakamakon gudummawar da ya bada a harkokin siyasar jihar, da kuma yadda ya rika manyan mukamai da suka hada da minista a lokacin Abacha da kuma sakataren gwamnatin tarayya a shekara ta 2007.

Leave a Reply