Home Labaru Sabon Kudiri: Gwamnatin Bayelsa Za Ta Rika Biyan Tsaffin ‘Yan Majalisa Kudin...

Sabon Kudiri: Gwamnatin Bayelsa Za Ta Rika Biyan Tsaffin ‘Yan Majalisa Kudin Fansho

224
0

Majalisar dokoki ta jihar Bayelsa, ta amince da biyan ma’aikatan ta wasu kudade a matsayin na fansho bayan sun bar majalisa.

Dan majalisa Peter Akpe ya gabatar da kudurin a zauren majalisar, wanda ya tanadi a biyan shugaban majalisa naira dubu 500 duk wata a matsayin fanshon sa bayan ya bar majalisa.

Haka kuma, kudirin ya bukaci gwamnatin jihar ta biya mataimakin shugaban majalisar naira dubu 200 duk wata a matsayin fansho bayan ya bar aiki, yayin da dokar ta nemi a biya sauran ‘yan majalisa naira dubu dari-dari a kowane wata.

Bugu da kari, dokar ta sa tsofaffin ‘yan majalisar jihar a cikin wadanda za su ci gajiyar tsarin, yayin da asalin ‘yan majalisar da su ka wakilci al’ummar su kafin samar da jihar Bayelsa za su amfana da sabon tsarin.

Yanzu haka dai, ana jiran gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya sa hannu a kan kudurin don ya zama doka, sai dai al’umma da dama sun nuna rashin amincewar su da wannan kuduri.

Leave a Reply