Home Labaru Badakalar Diezani: An Daure Jami’in Hukumar Zabe Shekaru 6 A Gidan...

Badakalar Diezani: An Daure Jami’in Hukumar Zabe Shekaru 6 A Gidan Yari

361
0
Diezani Alison Madueke , Tsohuwar Ministar Man Fetur

Wata babbar kotu da ke zama a garin Gumel na jihar Jigawa, ta daure wani mataimakin darakta a hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa Auwal Jibrin tare da abokin aikin sa Garba Isma’ila tsawon shekaru 13 a gidan yari.

Mai sharia Yusuf Birnin Kudu ya yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan ya kama su da laifi a kan tuhume-tuhume shida a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke ce ta yi rabon sama da dala miliyan 115 a lokacin zaben shekara ta 2015, daga cikin kudaden ta rabar naira miliyan 250 a jihar Jigawa, inda Auwal da Garba su ka samu naira miliyan 45 daga ciki. Alkalin kotun dai ya yanke wa mataimakin darakta Auwal Jibrin hukuncin daurin shekaru 6, yayin da abokin sa Garba ya samu hukuncin daurin shekaru 7, kuma kotun ta umarci hukumar EFCC ta kwace duk kudade da kadarorin da su ka saya da kudin, amma banda wani gida guda da ke garin Birnin Kudu.