Home Labaru Tartsatsin Wuta Ya Haddasa Rarraba Lantarki – TCN

Tartsatsin Wuta Ya Haddasa Rarraba Lantarki – TCN

327
0

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya TCN, ya bayyana cewa matsalar rashin wutar lantarki da aka fara fuskanta ta faru ne saboda jijjigar maganadisun wutar lantarki da ya afku.

Kamfanin ya ce jijjigar wadda ta faru a ranar Lahadin da ta gabata, ta haddasa tashin tartsatsin wuta a babbar tashar lantarki ta Benin, hedikwatar jihar Edo.

Kakakin kamfanin Ndidi Mbah, ta ce hakan ya haddasa tashin wuta a babbar tukunyar na’urorin tara karfin lantarki da ke yankin.

Ndidi Mbahy ta tabbatar da afkuwar matsalar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce matsalar tashin wutar ta afku da misalin karfe 9:10 na safiyar Lahadin da ta gabata.