Home Labaru Kiwon Lafiya Babban Laifi: Wata ‘Yar Najeriya Ta Yi Kokarin Harbe Wani Dan Sanda...

Babban Laifi: Wata ‘Yar Najeriya Ta Yi Kokarin Harbe Wani Dan Sanda A Italy

386
0

An kama wata ‘yar Najeriya mai suna Blessing Rapuruchukwu Okafor, mai shekaru 31 a duniya da miyagun kwayoyi a Tasahr jiragen sama na Trevisto, da ke kasar Italy.

Rahotanni sun nuna cewa Blessing ta na daya daga cikin bakin hauren da suka shiga kasar Italy ta kasar Libya, inda ake tsallakawa da su ta teku a jirgin ruwa.

Blessing, ta yi kokarin harbe dan sanda da ya kamata ne bayan zuwan su asibitin sai aka kai ta bandaki domin ta amayo da kwayar dake cikin na ta, sai ta yi kokarin kashe jami’in dan sandan.

 A cewar jami’in dan sandan, wacce ake zargin, ta kwace bindigar da ke jikin shi, inda ta yi kokarin harbin shi da ita, sai dai kuma cikin rashin sa’a ba ta san cewa bindigar a kulle ta ke ba, inda ta dinga harbawa amma ta ki tashi.A lokacin ne shi kuma jami’in dan sandan da taimakon ‘yan uwansa suka yi kokari wurin kwace bindigar daga hannun wacce ake zargin.

Leave a Reply