Home Labaru Abubuwan More Rayuwa: Al’ummar Karamar Hukumar Gada Na Kokawa

Abubuwan More Rayuwa: Al’ummar Karamar Hukumar Gada Na Kokawa

427
0

Al’ummar da ke karamar hukumar Gada a jihar Sakkwato, sun koka akan matsalolin abubuwan more rayuwa a yankin .
Mai magana da yawun al’ummar Gada, Alhaji Abdulwahab Liman Aliyu, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai a Kaduna, kan matsalolin da al’ummar wannan yanki ke ciki.
Ya ce duk da cewar suna bayar da gudunmuwa da goyon bayan da suka dace ga mulkin dimukuradiyyaramma yankin su na cikin mawuyacin hali, inda ya bukaci gwamnatin jihar Sakkwato da ta karamar hukumar Gada da kuma sauran ‘yan siyasa su duba halin rayuwa da suke ciki, su kawo musu dauki.
Alhaji Abdulwahab, ya ce sauran matsalolin da suke fuskanta sun hada da rashin ingantaccen hanya da ta hada garin Tabannin Saddi da sauran garuruwa da ke karamar hukumar Gada.
Ya ci gaba da cewar, rashin wannan hanya a duk lokacin da wani a karamar hukuma ta Gada ba shi da lafiya, a na fuskantar matsaloli ma su yawan gaske .