Wani likita ya sanyawa manyan mutane guda 90 da kuma yara kanana 65 cutar nan mai karya garkuwan jiki a kasar Pakistan ta hanyar amfani da sirinjin allurar da ya gurbata,.
Wani jami’in ‘yansandan dake jagorancin sharia’r a kudancin birnin Larkana, Kamran Nawaz ya ce sun kama wani likita bayan sun karbi korafe-korafe daga hukumomin lafiya.
Jami’in ‘yan sandan ya ce an fada masu cewa likitan na dauke da cutar” an fara fadakar da hukumomi game da al’amarin a makon da ya gabata, bayan da aka sami yara 18 dauke da cutar sakamakon gwaji da aka yi.
Wani jami’in kula da lafiya a gundumar Dr. Abdul Rehaman, ya fada wa kamfanin dillancin labaran faransa cewa sama da mutane 90 aka samu dauke da cutar, kuma yawan kananan yara ya kai 65.Ana ganin kasar Pakistan a matsayin kasar dake da karancin yaduwar cutar.