Home Labaru Ba Za Mu Amince Da Hatsaniya Ranar Rantsar Da Gwamnan Kano Ba...

Ba Za Mu Amince Da Hatsaniya Ranar Rantsar Da Gwamnan Kano Ba – Cp Gumel

77
0

Rundunar ‘yan Sandata Jihar Kano ta tabbatar da cewa, ba za
ta amince duk wani nau’i na kawo tashin hankali ko tarzoma a
wajen bikin rantsar da gwamnan jihar Kano da sauran ‘yan
majalisar jiha da tarayya ba.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘yan sanda na jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa ya raba wa manema labarai.

Sanarwa ta ce, kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya kuma ja kunnen dukkan magoya bayan jam’iyyu da iyayen gidan su a kan batun tsatsauran ra’ayi na siyasa don su janye mummunar aƙidar su.

CP Usaini Mohammed Gumel ya ƙara da cewa, duk masu niyyar yi wa jihar Kano zagon ƙasa su ƙoƙarta su janye wannan mummunan ra’ayi.

Ya ce za su cigaba da gudanar da aiki a dunƙule da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da kwanciyar hankali da kare kadarorin jama’a da gwamnati, tare da ganin an samu nasarar gudanar da bikin rantsar da gwamnan jihar Kano da sauran ‘yan majalisar jiha da wakilai cikin ƙoshin lafiya.

Leave a Reply