Home Labaru Kiwon Lafiya Shekaru Biyar Za A Kwashe A Jere Ana Fama Da Tsananin Zafi-...

Shekaru Biyar Za A Kwashe A Jere Ana Fama Da Tsananin Zafi- Bincike

46
0

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, shekarun 2023
zuwa 2027 za su kasance masu tsananin zafin da ba a taɓa
samu ba a tarihi, sakamakon yadda tururi mai gurɓata muhalli
ke ci-gaba da yawaita.

Ƙwararrun majalisar a kan yanayi sun ce, duniya za ta ga shekaru biyar a jere da za a yi tsananin zafin da ke da nasaba da ɗumamar yanayi.

Bayan wani taro da tawagar ƙwararrun ta gudanar biyo bayan dogon bincike game da tsananin zafin da duniya ke gani, sun ce cikin shekaru biyar masu zuwa akwai hasashen yiwuwar a iya samun shekara guda maras tsananin zafi.

Kafin wannan bincike na ƙwararrun dai, shekara ta 2015 zuwa 2022 ne ke matsayin shekaru mafi tsananin zafi da duniya ta gani, yayin da zafin na wannan karon ke ƙoƙarin zarce wanda aka gani a waɗancan shekarun.

Kƙwararrun sun kara da cewa, shekara bayan shekara tsananin zafin zai cigaba da rubanyawa matuƙar ba a sauki matakan da su ka dace wajen rage fitar da tururi mai guba da manyan ƙasashe masu masana’antu ke yi ba.

Leave a Reply