Home Labaru Ayyukan Ta’addanci: Sama Da ‘Yan Nijeriya 20,000 Sun Tsere Zuwa Nijar –...

Ayyukan Ta’addanci: Sama Da ‘Yan Nijeriya 20,000 Sun Tsere Zuwa Nijar – UNHCR

314
0

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tashin hankalin da ake samu na ‘yan bindiga a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina, sun tilasta wa mutane akalla 20,000 tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar don samun mafaka daga watan Afrilu zuwa yanzu.

Kakakin hukumar Babar Baloch ya shaida wa manema labarai cewa, rikicin ‘yan bindigar ba ya da nasaba da Boko Haram, sai dai mutane na tsere wa hare-haren ‘yan bindiga ne saboda dalilan da su ka hada da rikicin makiyaya da manoma da mai nasaba da kabilanci da kuma masu garkuwa da mutane.

Baloch, ya ce matsalar ta fi kamari a Jihar Zamfara, wadda ta haifar da rasa dimbin rayuka da asarar tarin dukiya.

Hukumar ta ce, wannan ya na daga cikin dalilin da ya sa gwamnatin Nijeriya ta haramta hakar zinare a jihar Zamfara, saboda zargin cewa masu aikin su na taimaka wa tashin hankalin da ake samu.

Leave a Reply