Home Labaru Yaki Da Rashawa: Shari’ar Babangida Aliyu Da Nasko Ta Dauki Sabon Salo

Yaki Da Rashawa: Shari’ar Babangida Aliyu Da Nasko Ta Dauki Sabon Salo

303
0

Wata babbar kotun Tarayya da ke Minna, ta umurci kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja ya gurfana a gaban ta, sannan ya bada jawabi a kan rashin aiwatar da umurnin kama tsohon gwamnan jihar Babangida Aliyu da Umar Nasko.

Alkalin kotun Mai shari’a Aminu Aliyu ne ya umurci kwamishinan ‘yan sandan ya gurfana tare da masu laifin guda biyu a ranar 13 ga watan Yuli.

Wata majiya ta ce, Babangida da Nasko sun kai lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bada domin gurfana a kotu ranar 23 ga watan Mayu, bisa zargin karkatar da kudi kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 900 amma su ka kasa bayyana, lamarin da ya sa mai shari’a Aliyu ya bada umurnin a kamo su.

A lokacin da lamarin ya taso, wadanda ake zargin sun gaza bayyana a gaban kotun, amma lawyan tsohon gwamnan Olajidele Ayodele ya halarta, inda ya ce zai tabbatar da cewa ya sanar da Babangida Aliyu a kan kwanan watan da za a sake zama wato 13 ga watan Yuli.

Leave a Reply