Home Labaru Garkuwa Da Mutane: Gwamna Masari Ya Nemi A Daina Biyan Kudin Fansa

Garkuwa Da Mutane: Gwamna Masari Ya Nemi A Daina Biyan Kudin Fansa

358
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bukaci al’umma su dakatar da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansar mutanen da su ka sace.

Masari ya bayyana haka ne, bayan ganawar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin arewa a fadar sa da ke Abuja.

An dai yi ganawar ne, domin tattauna matsalar rashin tsaro da yawan sace-sacen mutane musamman a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.

Yanzu haka dai shugaba Buhari ya sake bada tabbacin jaddada tsayuwar daka wajen samar da ingantaccen tsaro a fadin Nijeriya.

Gwamnonin da su ka halarci taron kuwa sun hada da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, da Kashim Shettima na jihar Borno, da Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, da Aminu Bello Masari na jihar Katsina, da kuma Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto.

Leave a Reply