Home Labarai Arangama Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Jigawa

Arangama Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Jigawa

66
0
Heders clash
Heders clash

Akalla mutum uku ne suka jikkata yayin da manoma da makiyaya suka yi arangama a dajin Baranda.

Kakakin rundunar DSP Lawal Shiisu ne, ya tabbatar da hakan inda ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a ranar Talata.

Ya ce da samun rahoton, babban jami’in ‘yansanda na sashen Kiyawa, tare da tawagar ‘yan sintiri,

suka garzaya wajen tare da tawagar ta hada da jami’an karamar hukumar Kiyawa, da shugabannin Kautal Hore da Miyetti Allah,

da kungiyar manoman Nijeriya (AFAN), da shugabannin kauyen da abin ya shafa.

A yayin tattaunaw, rundunar ta gano mutane uku da suka jikkata tare da ceto wasu shida da ake shirin kai wa hari.

DSP Lawal Shiisu ya kara da cewa an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti inda aka yi musu magani.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu makiyaya biyu na da hannu a harin, amma rundunar za ta gayyace.

Leave a Reply